Kamfanin dillacin labaru na Nijeriya ya rawaito cewar garin Lori-Oke cikin Ogotun dake jihar Ekiti yayi cikar kwari da jama'a sakamakon labarin da ya bazu na wata akuya da ta haifi wani da mai kama da bil-adama.
Mai magana da yawun dagacin
garin, Sunday Ogunmeji ya bayyana cewa akuyar ta dauki tsawon lokaci tana
nakuda wanda ya wuce kima, sai da Fasto Daniel Odedele ya agaza aka ciro dan.
"Ta dauki dogon lokaci
tana fada, saboda haka fasto ya ji tausayinta ya taimaka mata dan ya
fito."
"Jaririn yana da duk
wasu gabbai da bil-adama yake dasu misali, fuska, hannu, da mazakuta. Yana da
kafafu biyu da hannu kowanne da kofato da a jiki." Inji Sunday
To amma sakamakon cunkuson
jama'a da ke tururuwar kallon wannan halitta bai jima ba ya ce ga garinku.
Wani dan acaba ya fadawa
majiyar cewa koda akuyar ta dubi abinda ta haifa nan take ta arce tana bololo
ta shiga jeji. Sai da zaratan matasan kiyaye zaman lafiya suka bazama sannan
suka samo ta da kyar.

No comments:
Post a Comment