Mutuwar tsohon Shugaban kasar Afirika ta kudu
na ci gaba da sanya Shugabannin kasashen duniya kuka.
An samu rahoton mutuwar ne daga Shugaban Kasa Zuma wanda cikin alhini ke bayyana cewa " Yau duniya ta yi asarar danta, yayin da kasarmu ta rasa uba, a yau mun kasance marayu na hakika."
Shi kuwa Shugaban kasar Amurka Barak Obama cewa ya yi " Duniyarmu ta k'ank'ance saboda rashin Mandela. Nelson gwani ne wajen gudanar da sha'anin mulki, dukkanmu muna kwaikwayonsa ne".
Rahotannin da mu ke samu sun tabbatar da cewa a ko wanne waje cikin fadin kasar an dakatar da harkokin walwala da na kasuwanci, yayin da jami'an tsaro suka halaktawa kansu cire huluna su ke yawo haka......
Mandela dai ya shafe tsawon shekaru 27 a gidan firsina dalilin gwagwarmayar k'watar 'yancin k'asarsa kafin ya zama shugaban kasa.
An bayyana shi da cewa Shugabane mai adalci da kishin al'ummarsa, ya mutu a yayin da ya ke shekaru 95.

No comments:
Post a Comment