BABU MASU AIBATA MINISTER YERIMA SAI
'YAN ADAWA MASU YARFEN SIYASA
Dr.
Yerima Lawal Ngama dan asalin jihar Yobe a garin Gashua, Kamar yadda kowa ya
sani sunansa ya shahara ne a fagen aikin banki musamman a bangaren kasafin
kudi, ko da ya ke dama ya yi digirinsa na farko a kan aikin Akawu a Jami'ar
Maiduguri, ya sake yin digirinsa na biyu a fannin Akawu da kasafin kudi, a
Jami'ar Glasco da ke kasar Ingila, ya yi digirinsa na uku a fannin kididdigar
kudi da kasafinsu a Jami'ar Birmingham da ke kasar Ingila.
An
ruwaito cewa minista Ngama mutum ne mai kwakwalwa tun yana karamin yaro, bai
taba wuce mataki na uku a ajinsu ba, ya tab'a karbar lambar girma na Zakaran
dalibi a Gashua Central Primary School a 1973. Ya sake karbar kyautar dalibin
d'alibai a Govt Secondary School Gashua a 1978. Ya sake karbar kambun karramawa
ma fi girma wanda ya rubuta kundin bincike a 1990 a Jami'ar Birmingham a kasar
Ingila. Babban bankin Najeriya ya karramashi da kambun girmama basirarsa a
1991. Haka Diamond Bank wanda ya karrama shi har a karo na biyu. An bayyana
cewa ministan ya fara da aikin koyarwa ne a Jami'ar Maiduguri fannin tsimi da
Akawu, har zuwa lokacin da ya zama babban malami a sashen, ya yi zaman bincike
a Tulane University, New Orleans a Kasar Amurka. Sannan ya yi aiki da Nigeria
Deposit Insurance Corporation a matsayin babban Manager a sashen tsare-tsaren
gudanar da bankuna. Dr. Yerima ya rike mukamai a bangarori da dama a 'Diamond
Bank' wanda suka hada da manajan shiyya-shiyya da shugaban gudanarwa da kuma
babban darektan harkokin walwalar jama'a. Kafin daga bisani ya sauya akalar aiki
zuwa First Bank in da a nan ya rike babban darektan na shiyyar Arewa.
An
tantance shi ne cikin rukunin wasu mutane da dama in da a ka tabbatar da
dacewarsa na zama ministan kudi, a wancan lokacin kuwa minista Ngozi ba ta bar
mukaminta na babban bankin duniya ba, a sannan ne kuma takaddama ta kaure wasu
na ganin Dr. Yerima ne ya fi cancanta ya zama babban minista yayin da wasu ke
ganin ai Ngozi ce ta fi dacewa.
Daga
bisani a ka yi maslaha a ka ba shi karamin minister ita kuma babba.
Sanin
kowa ne mulki ya na da wuyar sha'ani a Najeriya musamman wajen wadanda su ka
rike gaskiya da amana.
An
ruwaito cewa tun da minista Yerima Lawal Ngama ya kama aiki ya samarwa mutane
da yawan gaske aiki a fannoni da dama kuma yana tallafawa matasa wajen samar da
sana'o'i da ayyukan dogaro da kai. Kasancewarsa mutumne mai kaunar talakawa ya
zamto linzamin janyo duk wani aikin alheri daga gwamnatin tarayya zuwa yankunan
Arewa.
An
bayyana ministan a matsayin mai aikin gani a k'asa ba yawan surutu ba, nazari
da bincike sun nuna cewa ya na kishin al'umma fiye da yadda ya ke kishin
aljihunsa da muradunsa.
A
satin da ya gabata ya bayyana cewa da 'yan majalisar tarayya sun rattaba hannu
a kasafin kudin 2014 to, da al'amura sun saukaka ga al'ummar kasar nan Kuma da
ba a samu tsaikon gudanar da kasuwanci ba saboda walwalar kudi a hannun
al'umma. Wasu 'yan adawa tuni su ka juya wannan al'amari su ka fara sukar
wannan ra'ayi a wasu kafafen yada labarai, to, wani abu da Hausawa su ke cewa
Allah ke gadin shekar Tsuntsu ba iska ba in don ta iska ne da tuni ta yi
tafiyar yaji da shi. Wasu kuwa na cewa in Hasken Rana ya fito tafin Hannu ba ya
iya kare shi.
Mu
dai kullum cikin fatan alheri mu ke ga shugabanninmu na gari, wajen da su ka
kuskure Allah ya yi musu jagora zuwa hanyar haske.

No comments:
Post a Comment