Thursday, 12 December 2013

Wasikar Sanusi Lamido Zuwa Jonathan

Gaskiyar Magana Wasikar Sanusi Lamido Zuwa Jonathan.


Tun hawan Mallam Sanusi a kujerar Gwamnan Babban Bankin kasa muke ta shan surutai da maganganu daga wani sashe na kasar nan wadanda a wurinsu duk abunda Gwamnan ya yi ba dai-dai bane. Ko da ya ke duk kushe da hassadarsu sai dai su kakaba masa karya da sharri wanda wannan ba wani abun damuwa bane tunda a dimokuradiyya muke. Kowa yana da yanci ya fadi ra’ayinsa ko da shirmene kuwa.

Kowa ya san Mallam Sanusi baya ganin abubuwan da ba dai-dai ba ya kuma kama bakinsa ya tsuke. Duk inda ya ga ba dai-dai ba sai ya yi magana a kai.
Ya yi magana a kan irin dumbin kudaden da 'yan majalisar mu na tarayya su ke dumbuza a sunan albashi da alawus wanda ya kai kashi 25 na duk kudaden yau da kullum da Gwamnatin tarayya take kashewa.

Yan majalisar ba su ji dadin wannan ba saboda ya bayyana wa al’umma abunda ba sa so a bayyana. Hasali ma sun nemi a cire shi daga mukaminsa a inda shi kuma ya amsa musu da cewa in dai kan ya fadi gaskiya ne to su zo su amshi aikin domin shi bai dorawa kansa ba.

Haka kuma an ta yin ikirarin cewa Mallam Sanusi ya furta cewa gwamnatin tarayya ta hanzarta rage kashi 50 daga cikin ma’aikatanta in dai tana so ta samu kudaden da zata yiwa al’umma aiki. Wannan ba daidai bane.

A matsayin Gwamnan babban bankin kasa Mallam Sanusi shi ne da hurumin ya yi wa kasa bayanin halin da gwamnati ta ke ciki, inda kudaden gwamnati suke shiga da kuma gayawa al’umma abun da yake yi ko kuma yake gani ya kamata ayi dan a samu daidaiton arzikin kasa.

Kamar maganarsa ta yan majalisa, Mallam Sanusi bai ce a kori kowa ba amma ya fadi cewa kashi 70 na kudaden kashewa akan ma’aikatan tarayya a ke kashewa. Ba huruminsa bane ya koresu ko ya sa a koresu amma aikinsa ne ya gayawa mahukunta da al’ummar Najeriya yadda kasar take tafiya.

A wannan satin ne a ka samu wata wasika wacce a ke watsawa a kafafen yada labarai wacce Gwamnan ya rubuta zuwa ga shugaban kasa Jonathan Wasikar na dauke da ankararwa zuwa ga wasu makudan kudi da su ka bace wanda a kalla sun kai naira tirillion takwas a kalla dalar amurka 49.8 tsakanin ma'aikatar kudi zuwa ma'aikatar tace man fetur ta kasa wanda a ka dora alhakin hakan kan minister kudi Ngozi da Minister Desiney. A fayyace cikin wasikar akwai jadawalin kasafin kudin shiga da fita tsakanin babban bankin da da ma'aikatun, sai dai babu tabbacin Malam Sanusi ne ya rubuta takaddar saboda ba rattababben saka hannunsa a jiki.

Mallam Sanusi bai bar kowa ba domin a watan Disamba 2012 ya gargadi gwamnatin tarayya da ta rage azarbabin da ta ke yi wajen tara basussuka ba gaira ba dalili saboda yin hakan ba abunda zai haifar sai dorawa yan Najeriya wahalhalu iri-iri .

Ya tab'a kuka da yadda a ke ta amso basussuka da kudin ruwa mai tsada wanda za’a bar wa yayanmu da jikokin mu su zo su biya haka siddan.
Lokacin da Babban Gwamnan ya ke wannan kalami jimillar bashin da ke kan Najeriya a waje ya kai Dalar Amurka biliyan 6.2 a watan satumba 2012. Shi kuma bashin da ake bin ta na cikin gida ya tsaya akan Naira trillion 6.3.

Yan kwanakin nan aka shaida cewa yanzu bashin waje ya nausa zuwa Dalar Amurka biliyan 7.7 a inda na cikin gida ya haura Naira trillion 6.85. A kullum wannan ci gaba yake tayi kuma babu wani hange cewa za’a shawo kan wannan al’amari.

Haka kuma ya Kara matsa lamba akan cewa a tashi tsaye ayi maganin cin hanci da rashawa da yai wa wannan kasa katutu. Ya kula da cewa akwai alama ana sane aka bar masu rike da madafun mulki suke ta wadakala da kudaden al’umma yadda ransu yake so ba tare da jin tsoron komai ba.

Irin wadannan kalamai da maganganu su ka sa wandansu mutane wadanda suka daure wa karya gindi suke so su ga sun sauke shi daga mukaminsa na Gwamnan Babban Bankin Kasa. To amma a kan me? Akan wacce hujja? Saboda yana fadan gaskiya? Ko dan yana kyamatar yan aci bulus?

Abun da ya sa kenan yace musu shi ako wane lokaci su ke san aikinsu zai iya ajiye musu. Toh har zuwa yanzu kuwa ba wanda ya iya futo da wani laifi yace ga laifin Mallam Sanusi. Suna zaune kullum sai dai suji ana ta yi masa kyauta da yabo saboda ayyukan da yake yi wadanda sun canza gaba daya sashen hada-hadar kudicikin yan shekaru kalilan.

Hirar da a ka yi da Malam Sanusi a gidan talabijin na AIT ya bayyana cewa shi fa gyara ya zo yi kuma ya gyara abinda ya gyara, in ya kammala zangonsa to, ba zai nemi a sake ba shi zango na biyu ba. Wannan hira ta tsumani matuka saboda sanin amfaninsa ga kasar nan.

Ya samu kalubale lokacin da ya bayar da Naira miliyan 100 da kuma Naira miliyan 20 ga mutanen kano da Suleija wadanda masifar Yan Boko haram ta hada dasu. Wadansu suna ganin hakan bai kamata ba saboda akwai wadansu wuraren da suma wannan ko wata masifar ta fada musu amma ba’a basu komai ba. Shi kuma ya agazawa wadannan wurare ne ba dan daga kano yake ba sai dan cewa abun ya fi kazanta a wannan wurare. Kuma tabbas yana da muhimmanci a taimaka musu.

Duk da dai ana ganinsa kamar dan tada kayar baya ne, Mutane suna ganin ya gagari Shugaban Kasa Jonathan wajen tsayawa daram-dakam wajen akida kuma babu wani takamemen aikin da shugaban ya ke tinkaho da shi kamar aikin Malam Sanusi na fannin gyaran tattalin arzikin kasa saboda ganin irin ci gaban da a ka samu a karkashinsa ta hanyar daukan nagartattun matakai wanda duk duniya ke yaba masa. Wannan tasa a ke ganin shugaban kasar zai yi duk yadda zai yi dan ya ga cewa Mallam Sanusi ya yarda da ya sake maimaita wata shekara hudun a kan kujerar Gwamnan Babban Bankin Kasar.

Don a tabbatar da cewa an samu ci gaba kuma an dora a kan nasarar da a ka samu a baya ta shafe san zuciya da kan iya futo da kai a dai-dai irin wannan lokaci musamman ma da yake komai yanzu sai an sa siyasa da yan ubanci a ciki.

An tabbatar da cewa wannan dan taliki nan ya yi namijin aiki wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan tare da tsaftace sashin bankuna wanda da yake dab da rugujewa, a daidai lokacin da kasashen da suka ci gaba suke faman share gumi wajen neman hanyar da za su yi su fidda tasu kasar daga irin wannan dabdalar da ta samemu.

Mallam Sanusi tsayayye ne a kan aikin da ya ke yi kuma a shirye yake da yafuskanci ko wace irin matsala da kuma ko wane irin kalubale da yan adawa za su iya bujiro da shi. Ya san aikinsa na harkar banki kuma yana da sani matukar gaske wajen harkar tattalin arzikin kasa. Shi yasa ba inda za’a layance masa. Kuma duk wanda zai zo masa da wata magana sai yayi tunani sau biyu tunda duk ta inda ka futo yana kallonka.

Mallam Sanusi masani ne. Akwai karatun Al’qurani akan sa fiye da yadda ka ketsammani. Wannan shi yake taimaka masa wajen sanin bin ka’ida da yin abubuwa kamar yadda Allah Subhanahu Wata’ala yace mutum ya yi. Ban manta ba shekara biyu kenan yana yin tafsir lokacin azumi daga kasar Makka dan amfanin mahajjata.

In karatun bokon ne nan ma ba mai goga wa da shi domin ya karantu sosai. Turanci a bakinsa ko baturen Ingila sai dai ya sa masa ido. A duk lokacin da yake magana ko a gida ko a waje mutane na tsayawa su saurareshi ba dan turancin ba sai dan sun ga mutum wanda ya san abun da yake fada.
Maganarsa dutse ce. Shi yasa kungiyar hadin kan turawa ta bashi lambar yabokuma take gayyatar sa dan yaje ya yi wa mutanensu jawabi akan al’amura da suka kebanci tattalin arzikin kasa.

Kwamitin kudi ma na majalisar dattawa ta Amurka ita ma sai da ta gayyaci Mallam Sanusi zuwa Amurka dan ya yi wa yan kwamitin bayani akan yadda za’a yi maganin tabarbarewar arzikin bankuna. Tun da ake Gwamnan Babban Bankin Kasa a Najeriya ba wanda aka taba gayyata yaje ya ilmantar da wadannan turawanyadda za su yi maganin wata matsala. Sai dai su zo su nuna mana yadda zamu yi maganin wata matsalar ba dai mu muje mu nuna musu ba. Toh amma Mallam Sanusi ya yi an gani kuma an gamsu da cewa ya san aikinsa ciki da waje shi yasa suka kirashi. Wannan babbar karramawa ce kuma abun alfahari ga wannan kasa gaba daya.

Tun da ya fara aikin banki ba’a taba samunsa da wata almundahana, ko rashin gaskiya ko wani san rai ba har zuwa yau da yake kan kujerar Gwamnan Babban Bankin kasa. Abun da yasa kenan duk lokacin da yayi magana mutane gida da waje suna saurarensa. Kullum ana yi masa shedar cewa na Allah ne.

Ya fara jihadi a wannan kasa. Ba abunda yafi sai abar shi ya karasa aikinsa.Shekara hudu nan gaba zai tabbatar da cewa harkar kudi a kasar ta kai inda Najeriya zata goga kafada da kowace kasa anan duniyar ta hanyar futo da kuma bin tsari managarci. 
Ma’aikatan Babban bankin kasa suna jin dadin zamansa a wannnan mukami saboda sun ga yadda su kansu yai musu garanbawul, ya tabbatar musu da hakkinsu, ya dauki ma’aikata isassun yadda za’a yi aiki ba takura sannan ya tabbatar da cewa kowa ya san aikinsa ta yawan tura su kwasa-kwasai na cikin gida da ketare.

In da kuri’a za’a kada lallai ma’aikatan Babban Banki gaba daya za su jefa masa kuri’a dan ya ci gaba da wata shekara hudun.
Mallam Sanusi ya san abun da duniya ta ke ciki kuma yana da ilmin sanin abun da zai kai ya komo a hada-hadar cinikayya, tattalin arzikin kasa, tashi fadi na harkar banki da sauransu. Ya kware sosai wajen tsara yadda da sanin yadda kasuwarcanjin kudin kasar waje da kudin ruwa yake wakana.

Mun zabi Mallam Sanusi da ya ci gaba ne dan tabbatar da cewa ayyukan da yayi wajen shekara hudu baya ba su samu nakasu ba sai dai a samu karin ci gaba wanda zai tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar nan ya tsaya da kafafunsu daram. Tabbas in aka kawo wani yanzu za’a samu matsala inda sabon zuwan zai so ya kawo nasa tsare-tsaren wadanda kan kawo nakasu ga ci gaban da aka samu a baya.

Yan uba sun manta da halin da sashen kudi na wannan kasa yake kafin Mallam Sanusi ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin kasa. Sun manta inda bankuna suke ta rufewa ba kakkautawa, sun manta cewa masu sa hannun jari da dama sun tsere sun bar kasar dan su tsira da dan abun da ya rage musu bayan sashen hada-hadar hannun jari ya durkushe gaba daya.

Masana da dama a gida da waje sun ce kyakykyawan sanin yadda ake tafiyar da sashen banki na kasar shine zai sa Mallam Sanusi ya sake samun wata damar ya ja ragamar Babban Bankin kasar a karo na biyu.

Saboda bukatar da Najeriya ta ke da shi na ta gina a kan nasarar da aka samu a wannnan shekarun da suka shude inda duk wani abu da ya shafi harkar kudi aka yi masa garanbawul tun shekarar 2009 zai sa gwamnati ta rike abubuwa yadda suke dan kada ayi chanji kuma wata baraka ta bayyana.
Kowa ya fada Mallam Sanusi ya cancanci ya samu damar yin wata shekara hudun amma yanzu komai ya danganta da yadda Mallam Sanusi ya gani. Ba wanda ba ya kuskure sai Allah Subhanahu Wata’ala shi kadai. Mallam Sanusi kamar ko wane Dan Adam ba mamaki in ya yi kuskure a wani waje amma dole mutum ya yaba masa saboda karfin halinsa.

Kafin Mallam Sanusi Ya zama Gwamnan Babban Bankin kasa rarar kudin da aka samu daga saida danyan man fetur ya taimakawa waccen tsohuwar gwamnatin ta Babban Bankin kasa wajen turawa bankuna kudade wadanda daga baya aka yi almubazaranci da su. A wannan lokacin ana saida gangar danyan man fetur a kan Dalar Amurka 120.

A maimakon a samar da wani tsari wanda za’a jima ana samun alfanunsa sai aka bar wasu Manajojin Daraktocin masu bakar aniya suka shiga yar birin-birin da kudaden jama’a. A lokacin nan bankuna na ta faman turawa yan siyasa kudi wajen satar kuri’a lokacin zabe. In sun yi nasara dama ba wanda ya isa ya nemi a dawo da kudaden. In kuwa suka fadi zaben dama kudinsu ya kare wajen yakin neman zabe sai dai a kai su kotu daga inda za’a ta wasa da hankalin mutane amma ba za’a biya ba har abada.

Haka kuma a lokacin ne bankuna su kai ta bada basussuka dan mutane su sayi shares na bankunan da kafafuwansu ke rawa. Kullum ka duba jaridu sai rubuce-rubuce na karya akan ribar da banki ya samu. A lokacin ne ake samun bankuna masu wajen reshe uku a titi daya. Haka kuma za ka samu Manajojin daraktoci suna sayen jiragen sama da shelikofta da kudaden jama’a. Duk wannan kazanta ba wanda yai magana ballantana ya hanata har bankunan nan suka tunkuyi kasa.

Lokacin da tattalin arzikin kasa na duniya ya shiga rudani kowace kasa tana neman yadda za ta fita daga wannan kangin. Mutanenmu gani suke kamar wannan ba zai taba samun Najeriya ba. Shekara daya bayan wannan bankunan kasa suka fara korar mutane, suna kasa biya wa kwastamominsu bukatunsu. A wannan lokacin ne aka gano cewa yawancin bankunan da kyar suke numfashi. Sun ruga sun karye. Hasali ma dai daga wajen Babban Bankin kasa suke ranto kudi dan su rayu. Wannnan ribar da suke ta faman talla duk ta bogi ce

Ana cikin wannan rudun aka bawa Mallam Sanusi ragamar Gwamnan Babban Bankin Najeriya dan ya yai shara, kakkaba da farfado da wadannan bankunan. Haka kuma nauyi ya fada kansa da ya farfado da sashen hada-hadar hannun jari na kasa, ya daga tattalin arzikin kasa da sauransu.

Kafin wannan lokacin bashin da ake bawa sashen harkar noma kashi 3% ne kawai bayan an san cewa wannan sashe shine yake kawo wajen 40% GDP kuma shine ya kawo girman GDP da wajen 7%. 

Amma kuma kudade suna ta tafiya wajen yan kalo-kalo a wajen yin caca a sashen hada-hadar jari. Kasuwar tana faduwa aka shiga matsala saboda kudaden sun narke an yi asara.

Banda matsalar da aka samu a baya dama can akwai rashin ingantaccen shugabanci a bankunan wanda dama shine ummul’abaisin matsalar da bankunan suka shiga. Haka kuma akwai rashin bincike da sa ido daga bangaren Babban Banki da sauran jami’oin bincike na wannan kasa wanda hakan ne ya sa bankunan suka ci gaba da cin karensu ba babbaka.
Wannan da wadansu abubuwa suka kawo durkushewar bankuna a Najeriya. Akan wannan ne Mallam Sanusi ya fara aikinsa. Duk sauran abubuwan da suka faru baya da haka zuwa yanzu ya zama tarihi. Wani abu da yayi wanda kuwa ya shiga tarihin wannan kasa shine na kame duk manajojin daraktocin da suka kada bankunansu da kuma gurfanar da su a gaban kuliya dan a kwatowa al’umma guminsu.

Mallam Sanusi ya yi aiki ba dare ba rana, ba ji ba gani, ba sani ba sabo, babu dan Allah dan Annabi. In ka saci kudade ko ka yi almubazaranci da kudaden mutane tosai kayi amansu ko ka tafi fursuna.
A cikin duk wadanda a ke yawo da sunansu dan su amsa daga wajen Mallam Sanusi ba wanda yai fice ko yake da karfin da zai maimaita ko kuma ya dora wani abun a zo a gani a kan aikin Mallam Sanusi.

Tabbas abun alfaharin Mallam Sanusi na kawo zaman lafiya, daidaito, da tsafta za mu nakasu in har bai yarda ya koma wa’adi na biyu ba.
Najeriya ta zama daya daga cikin wuraren da masu sa hannun jari suke wawar san zuwa saboda samun gawurtattun bankuna, ingantaccen sashen hada-hadar hannun jari, daidaituwar farashin kudaden waje, daidaituwar farashin kudin ruwa da kudin adani na kasa a ketare wajen Dalar Amurka Biliyan 50.

An jima ba’a samu saukar hauhawan farashin kayayyaki a kasar nan ba sai da hawan Mallam Sanusi in da yanzu ya sauka zuwa kasa da lamba goma. Alkaluma sun nuna cewa a Afrilu 2013 yana kan kashi 9.1. ya sauko daga kashi 12.5a Lokacin da Mallam Sanusi ya fara aiki a shekarar 2009 yana kan 12.5 amma yanzu alkaluman gwaji a watan Afrilu 2013 sun nuna cewa ya sauko zuwa kashi 9.1. Wannan babban aiki ne daga Babban Gwamnan Babban Bankin.

Ya yi aiki iya karfinsa. An samu canji ta ko wane fanni. Ya samu yabo daga duk kewayen duniyar nan. In har Najeriya na son ta cimma burinta na zama daya daga cikin kasashe ashirin da suka fi kowa ci gaba a duniya kafin shekarar 2020 to, babu shakka sai ta roki Mallam Sanusi ya ci gaba a karo na biyu.

Ina tabbatar da cewa in har Mallam Sanusi ne ya rubuta wannan wasikar to babu shakka sahihancinsa ya tabbata don irin wadannan kudi in za a wawura kashe mu raba a ke yi, da wadanda su ka sato da wadanda za su rufa asiri, watakila ko sun kwankwasa sun ga ba za su iya ba ne, oho!

1 comment:

  1. Hon Gebi
    “I think Malam Sanusi Lamido Sanusi is to be congratulated for several reasons, one of which is for his being as bold as he was to come out not only to voice it out but to even have document that has been presented by the press alerting the president of this.
    “The Sanusi Lamido Sanusi that I know does not lie cannot lie; he does not have the luxury in lying; it is in his nature. He will tell you the truth and will damn the consequences, so if truly this document did originate from him by way of him writing, then it must be the truth, and I’m not being biased or anything. When he came on board, so many people did not believe in him because they didn’t even understand where he is coming from, but thanks to this individual,” he said.

    ReplyDelete